Tsohon kaftin na tawagar kungiyar kwallon kafa ta Ingila, dan wasan tsakiya na kungiyar DC United dake kasar Amurka, Wayne Rooney, ya kai ziyara babbar fadar Shugaban kasar Amurka Donald Trump (White House) dake Washington, bisa wata ziyara kan bikin Kirsimeti.
Dan wasan mai shekaru 33 da haihuwa ya samu ganawa da dan shugaban mai suna Barron, mai shekaru 12 da haihuwa wanda kuma mai sha'awar kwallon kafa ne, yana buga wasa wa kungiyar DC United na matasa, inda suka dauki hoto tare da Rooney a yayin da ya kai wannan ziyarar.
Rooney wanda ya ke da tarihin dan wasan da yafi zurara kwallaye a tsohowar kungiyarsa ta Manchester United, ya koma DC United ne daga Everton a watan Yuni.
Inda ya samu nasarar jefa kwallaye 12 a kungiyar ta DC, a wasanni da ya buga mata inda har suka kai ga buga (play-offs) a gasar LMS, a watan Nuwamba.
Cikin tawagar da suka rufa masa baya zuwa fadar ta White House har da mai dakinsa Coleen da 'ya'yansu hudu.