Dan wasan Arsenal Sokratis Papastathopoulos ya ce abokin taka ledarsa a kungiyar Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang zai iya cin kwallaye akalla 30 kafin kammala gasar firimiya lig na bana 2018/2019.
Dan wasan na tawagar kungiyar kwallon kafa ta kasar Gabon ya zurara kwallaye biyu a wasan da Arsenal ta lallasa Burnley daci 3-1, a gasar firimiya lig mako na 18 a ranar Asabar da ta gabata a filin wasa na Emirates.
Hakan ya bawa dan wasan Aubameyang mai shekara 29 da haihuwa damar kamo takwararsa Mohamed Salah na Liverpool, inda kowannensu ya ke da kwallaye 12 a raga cikin wasannin firimiya, da suka buga a bana mako na 18.
Ya zuwa yanzu Aubameyang ya zurawa Arsenal kwallaye 22 a wasa 31 da ya buga mata a bangaren firimiya lig tun bayan dawowar sa Emirates daga tsohowar kungiyarsa ta Borussia Dortmund dake kasar Jamus.