Dan Wasa Salah Na Kasar Masar Ya Sake Kafa Tarihi

Danwasan gaba na kasar masar mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Muhammad Salah ya sake kafa wani tarihi a kungiyarsa ta Liverpool, bayan da ya zurara kwallaye har guda uku a wasa daya tak, wanda suka lallasa Bournemouth da ci 4-0 a gasar firimiya lig mako na sha shida.

Wannan kwallaye uku da Salah, ya zura sune cikon kwallaye na 40 da ya
ci wa kungiyar ta Liverpool cikin wasanni 52 da ya fafata mata,hakan na nuni da cewa shi ne dan wasa na farko da yafi ci mata kwallaye masu yawa cikin wasanni kalilan a tarihin kungiyar.

Bayan haka Salah shine dan wasa na farko da ya sha wa Liverpool kwallaye uku a wasan da su kayi tattaki zuwa gidan wata kungiya, (Away Match)
tun bayan tsohon dan wasanta Luiz Suarez da yayi a shekarar 2014, kafin ya bar kulob din.

Bisa tarihin gasar firimiya lig na kasar Ingila kuwa, Alan Shearer ne kawai da Andy Cole, suka samu wuce gaban Salah ta hanyar cin kwallaye 40 cikin wasanni 45, da suka fafata wa kulob din su.

A kakar wasan bara dan wasan Salah shine na biyu, cikin wanda sukafi zurara kwallaye a manyan wasan Nahiyar Turai guda biyar, wanda suka hada da Laliga, Premier, Bundesliga, Ligue 1, da kuma Serie A, inda ya jefa kwallaye har guda 42, bayan haka kuma ya lashe kyaututtuka da dama a bara, ciki harda gwarzon dan wasan kwallon kafa ta Nahiyar Afrika.