Dan Wasa Pavard Zai Koma Gungiyar Bayern Munich

Dan wasan kasar Faransa Benjamin Pavard

Benjamin Pavard dan wasa mai tsaron baya na tawagar kwallon kafar kasar Faransa, zai koma kungiyar Bayern Munich ta kasar Jamus da cigaba da fafata wasa, ranar 1 ga watan Yulin shekara 2019, daga kulob dinsa na Stuttgart.

Dan wasan yana daya daga cikin 'yan wasan Faransa wanda suka lashe kofin duniya na 2018, da ya gudana a kasar Rasha.

Zai koma kungiyarne kan zunzurutun kudi har Yuro miliyan £35, bisa yarjejeniyar shekara biyar. Dan wasan Pavard mai shekara 22 da haihuwa ya taho Stuttgard daga kungiyar kwallon kafa ta Lille akan kudi Yuro miliyan 11, amatsyin mai tsaron baya.

A wasan da Faransa ta doke Argentina da ci 4-3 cikin gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha a shekara ta 2018, Pavard ya jefa kwallaye hudu daga cikin wanda kungiyar ta zura.