Dan Wasa Luka Modric Ya Lashe Kyautar Zakaran Turai

Luka Modric ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kudu maso yammacin Turai na shekarar 2018 (Athlete of the Year).

Modric dan kasar Croatia shi ne na biyu acikin jerin 'yan wasan kwallon kafa da suka samu kyautar a tarihi bayan Hristo Stoichkov, wanda ya taba zama gwarzon dan kwallon kafa na Nahiyar Turai a shekarar 1994.

Modric mai shekaru 33 da haihuwa ya samu maki 77, hakan ya bashi nasarar lashe kyautar a biki na 46, da kamfanin yada labarai na Bulgaria (BTA) ke gudanarwa, inda ya doke Novak Djokovic wanda ya lashe kyautar sau biyar ajere, tun daga 2011 zuwa 2015.

Dan wasan Modric ya samu kyaututtuka da dama a wannan shekara, kama daga kyautar Ballon d'Or ya kuma ci kofin zakarun Turai da na zakarun Nahiyoyin Duniya a kungiyrsa ta Real Madrid.

Bayan haka ya taimaka wa kasarsa Croatia ta kai wasan karshe a kofin duniya, na shekarar 2018 da aka kammala a Rasha, inda suka kare a matsayi na biyu bayan da Faransa ta doketa da ci 4-1 ya kuma zamo gwarzon gasar.