Kungiyar kwallon kafa ta Porto, ta bada tabbacin cewar dan wasa mai tsaron ragarta Iker Casillas, na fama da cutar bugun zuciya.
Rahotanni sun bayyana cewar dan wasan Iker Casillas, ya fadi ne a yayin da suke atisaye da tawagar kungiyar ta Porto a karkashin jagoranci mai horaswa Sergio Conceicao, a ranar Laraba da ta gabata kafin daga nan aka daukeshi zuwa Asibiti.
Dan wasan mai shekaru 37, da haihuwa wanda ya fafata a mafi akasarin wasansa a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, kafin ya dawo kungiyar ta Porto, yanzu haka an kebe shi a wani Asibiti inda ba'a barin wasu su ganshi, sai dai Likitoci kawai, amman Likitocin sun bada tabbacin cewar Casillas yana samun sauki sosai.
Manyan takwarorinsa 'yan wasa na kungiyoyin kwallon kafa a Duniya, da suka hada da Cristiano Ronaldo, Leonal Messi dama tsohowar kulob din sa Real Madrid sun aika masa da sakon samun sauki bisa wannan cuta da yake fama da ita.