Hukumar kula da wasan kwallon kafar Ingila ta kasar Ingila (Football Association) ta rubuta wa kungiyar Manchester City wasika, don kokarin jin ta bakinta game da sakon Twitter da Bernardo Silva ya wallafa.
Silva ya kwatanta abokin wasansa Benjamin Mendy da wani hoton jikin
wata 'yar matumbirar agwagwa da kamfanin alawa ke amfani da ita a jikin jakar alawar da ake sayarwa a Portugal da kuma kasar Spain.
Tuni dai kungiyar masu gangamin yaki da wariyar launin fata ta Kick It Out ta yi kira ga hukumar (FA) da ta dauki mataki bayan hukumar ta tabbatar da
cewa tana binciken lamarin domin ranta ya baci sosai.
Silva ya wallafa sakon ne da karfe 12:44 agogon Nijar, Najeriya ranar Lahadi amma sai yayi sauri ya goge.
Daga baya ya sake wallafa cewa, "ai nufinsa wasa ya keyi da abokin sa, shi ke nan" mutum ba zai yi wasa da abokinsa ba ke nan.
'Yan wasan biyu Mendy da Silva abokai ne na kusa kuma sun yi wasa tare a kungiyar Monaco kafin dukkaninsu su koma City a 2017.