Dan Wasa Arjen Robben Yayi Murabus Daga Taka Leda

Dan wasan gaba na Bayern Munich Arjen Robben mai shekaru 35, da haihuwa ya ajiye takalman taka ledarsa bayan ya shafe shekaru goma yana murza mata tamola.

Dan wasan Robben ya ce zuciyasa ta dade tana son yayi ritaya, sai dai jikin yana ce masa a'a, ba yanzu ba don haka wannan shine hukunci mafi wahala da ya yanke wa kansa a tarihin kwallon kafar sa, inda ranar 30 ga watan Yuni 2019 kwantaragin sa da kungiyar Munich ta kare.

Dan wasan ya buga wa kasar sa ta haihuwa Holland wasanni 96, ya jefa kwallo 37, sannan ya taimaka wa kasar takai wasan karshe a gasar cin kofin duniya a shekara ta 2010, haka zalika ya taimaka musu suka kammala a matsayin na uku a gasar bayan shekara hudu.

A lokacin da yake buga wasa a kulob din Chelsea a karkashin kocinta Jose Morinho, a shekarar 2005, da 2006, ya lashe kofin Firimiya Lig na Ingila, sau biyu daga bisani ya koma Real Madrid ya lashe kofin La Liga na Spain.

Kafin ya bayyana ritayansa Robben ya lashe gasar Bundesliga sau 8, da kuma German Cup sau 5, sai kofin zakarun turai UEFA Champions League a shekarar 2013, duk da tawagar Bayern Muniich, ya jefa kwallaye 144 a cikin wasanni 309.

Tun kafin wannan lokaci Robben ya riga ya yi ritaya daga buga wa kasar sa Holland, wasan tun shekara ta 2018.