Atiku Abubakar Ya Kada Kuri'arsa A Jimeta A Jihar Adamawa

Dan takarar babbar jam’iyar adawa ta PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kada kuri’ar sa tare da daya daga cikin matansa Titi Atiku Abubakar, a runfar zaben.

Kamar sauran sassan Najeriya, a jihar Adamawa ana gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, inda shima dan takarar babbar jam’iyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar shima ya kada kuri’arsa.

Tun da sanyin safiya ne jama’a suka soma tururuwa zuwa runfunar zaben domin su kada kuri’a, an kuma girke duba jami’an tsaro musamman 'yan sanda da suke shawagi don tabbatar da doka da oda.

Kamar sauran masu kada kuri’a shima dan takarar babbar jam’iyar adawa ta PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kada kur’ar sa, shi da daya daga cikin matansa Titi Atiku Abubakar, a runfar zaben ta Ajiya Unit 0012, dake cikin Jimeta, a fadar gwamnatin jihar Adamawa, inda ya samu rakiyar magoya bayansa.

Muhammad Iliyasu Gamawa na cikin jami’an sa ido na wata jam’iya, ya bayyana yadda aikin ke tafiya ya zuwa yanzu.

Kawo yanzu rahotanni daga wasu sassan jihohin Adamawa da Taraba, na cewa an dan samu jinkiri a wasu mazabun, kamar yadda wani ya tabbatar min daga Gindin dorawa a jihar Taraba. A halin yanzu ana ci gaba da kada kuri’a a wasu runfunar zaben dana ziyarta.

Wakilin Muryar Amurka, Ibrahim Abdula'ziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Dan Takarar Babbar Jam'iyyar Adawa Ta PDP, Atiku Abubakar Ya Kada Kuri'arsa