Dan Takar Jam'iyyar Adawa A Congo Yace Bai Yarda Da Sakamakon Zabenba

Dan takarar shugaban kasa a Jamhuriyar dimokradiyyar Congo da ya zo na biyu a zaben da aka yi ranar 30 ga watan Disambar da ya gabata ya yi watsi da sakamakon zaben da aka fidda a hukumance, wanda ya nuna Felix Tshisekedi ne ya lashe zaben, yana mai kiran sakamakon shirme.

A yau Alhamis hukumar zaben kasar ta CENI, ta sanar da cewa Tshisekedi ya lashe zaben da kashi 38 cikin 100 na kuri’un da aka kada, abin da ya ba wakilan da ke sa ido akan zaben mamaki bayan da ra’ayoyin jama’a kafin zabe suka nuna cewa dan takarar jam’iyyar adawa Martin Fayulu shi ne zai ci zaben.

Fayulu, wanda ya sami kashi 34 cikin 100 na kuri’un, ya zargi hukumar zaben da yin magudi, ya kuma yi kira ga cocin Katolika ta kasar da ta fidda sakamakon da ta tattara. Jami’an diflomasiyya da dama sun fadawa kafafen yada labarai cewa kuri’un da tawagar wakilan Cocin suka kidaya sun nuna cewa Fayulu ne ya lashe zaben.

Shi ma ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian na da shakku akan sakamakon zaben, ya fadawa gidan talabijin din CNews a yau Alhamis cewa sakamakon zaben da aka fidda a hukumance bai yi daidai da ainihin adadin da aka kirga ba.