Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayyar Najeriya ta kama dan majalisar da ya ci zarafin wani direba a Abuja.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Josephine Adeh, ta tabbatar da cewar Alex Mascot Ikwechegh “na fuskantar tambayoyi a caji ofis din ‘yan sanda na unguwar Maitama”.
A cewar sanarwar da rundunar ta fitar a yau Litinin, direban bolt Stephen Abuwatseya ne ya shigar da korafi kan batun ga rundunar.
“Rundunar ‘yan sandan ta Abuja ta bayyana damuwa da halin rashin mutuntawar da Honorabul Ikwegh ya nuna kan mukamin babban sufetan ‘yan sandan Najeriya sanadiyar afkuwar lamarin.
Bayan zargin marin direban, rahotanni sun bayyana cewar ya furta kalaman raini na cewa, “kaje ka kira babban sufetan ‘yan sanda,” abinda ke alamanta rashin ganin hukumomin tsaro da kima.
Rundunar ta kara da cewa, kwamishinan ‘yan sandan Abuja, Olatunji Disu, ya bada umarnin gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.