Wani dan kunar bakin wake ya kutsa da motarsa cikin sojojin dake duba ababen hawa a Birnin Benghazi kasar Libya.
Ya kashe akalla sojoji bakwai
Wani rahoto yace mutane biyu ne ke cikin motar.
Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai wannan harin to amma ana kyautata zato mayakan sa kai ne masu kishin Islama suka kai harin.
Dama mayakan Islaman sun kwace babban Birnin kasar inda suka kafa tasu gwamnatin suka kuma tilastawa gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita ficewa zuwa gabashin kasar.
Harin na jiya Talata yazo ne daidai lokacin da wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman akan Libya, Berardino Leon ya kawo shawarar kafa gwamnatn hadin gwiwa a kasar.
Shawarar tashi wani kokari ne na kawo karshen abun da ya kira dagulewar yaki.
Tashin hankali da rikicin siyasa sun addabi kasar ta Libya tunda aka hambare aka kuma ksashe shugaba Moammar Gadahafi a shekarar 2011, mutumin da ya kwashi shekaru da dama yana yiwa kasar mulkin kama karya.