Yevgenia kara-Murza, ta fada jiya Talata cewa, likitoci sun ce sun gano wani abu cikin jikin mijinta da ya haddasa dakatar da aiki na galibin abunda ke cikin jikinsa. A makon jiya ne al'amarin ya auku. Koma bayan lafiyar dan jaridar, wadda rahotanni suka ce ya auku ne sa'o'i kamin ya bar kasar kan hanyarsa ta zuwa Amurka, ya tilastawa likitoci su dauki mataki mai gauni gameda dan jarida Vladimir, wanda dan shekaru 35 ne da haifuwa.
Matarsa tace, an dauki samfirin jininsa, da gashi da duka wasu sassan jiki da za'a iya gane ko an sakawa mutum guba, an tura zuwa kasashen ketare, ciki harda wata cibiyar bincike mai zaman kanta dake Isra'ila.
A birnin Washington, Senata John McCain, wanda ya juma yana cikin jerin masu sukar shugaban Rasha Vladimiri Putin, ya bayyana takaici kan lafiyar Kara-Murza, daga nan yayi hannunka mai sanda kan yiyuwar fadar Kremlin tana da hanu a rashin lafiyar dan jaridar.