Wani mai magana da yawun fadar gwamnatin kasar Rasha ya fada yau Alhamis cewa Rasha ta yi murna da jin dan jarida Arkady Babchenko, na raye, amma kuma labarin mutuwarsa na jabu abin mamaki.
An sami rahoton harbin sanannen dan jaridar mai bada rahotanni akan yaki, mai sukar gwamnatin Kremlin kuma ranar Talata a matakalar benen gidansa dake Kyiv. Amma sai ga Bobchenko ya ba ‘yan jarida mamaki a lokacin da ya bayyana lami lafiya jiya Laraba, yayinda jami’an tsaron Ukraine suka bayyana labarin mutuwarsa a matsayin na jabu don a ceci rayuwar dan jaridar.
Mai magana da yawun fadar Kremlin, Dmitry Peskov, ya fada yau Alhamis cewa bai san ko sakamakon wannan matakin ya cancanta ba, kuma abinda ya faru bai canza yadda Rasha ke kallon Ukraine, a matsayin kasa mafi muni ga ‘yan jarida ba.
Kungiyar da ke kare ‘yan jarida ta kasa-da-kasa ta yi Allah Wadai da labarin mutuwar Bobchenko, na karya, tana mai cewa “abin tada hankali ne, na da-na-sani kuma” a ce dakarun tsaron Ukraine, suna wasa da gaskiya.