Jami’an gwamnatin kasar Somaliya sun ce wani d’an k’unar bak’in wake ya ragargaza kan shi da boma-bomai a k’ofar Fadar shugaban k’asar.
Jami’ai sun ce a yau litinin d’an harin k’unar bak’in waken ya yi k’ok’arin shiga Fadar a daidai lokacin da wani ayarin motocin sojojin k’asashen Afirka masu tsaron zaman lafiya ya kai ga wata k’ofar shiga Fadar. Jami’an sun ce sojojin kiyaye zaman lafiyar sun bud’e wuta a kan d’an k’unar bak’in waken wanda a wannan lokacin ya farfasa boma-boman da yake rataye da su, sannan ya mutu.
Fadar na daga cikin ‘yan wurare k’alilan da ke hannu gwamnatin k’asar Somaliya wadda k’ungiyar k’asashen Afirka da Majalisar D’inkin Duniya ke baiwa goyon baya.
‘Yan gwagwarmayar Islama ne ke ta k’ok’arin hamb’are shugaba Sheikh Sharif Sheikh Ahmed da nufin kafa wata k’asa mai bin tsantsar tsarin mulkin Shari’ar Musulunci.