A cikin hirarsu da Sashen Hausa, Mista Boafo ya bayyana cewa, yana da sha’awar ganin ci gaban al’umma kuma ya yi aiki da ‘yan siyasa a matakai dabam dabam da ya kara mashi sanin hanyar tafiyar da jama’a.
Ga bayanin da ya yiwa Alheri Grace Abdu a hirarsu da shi.
An birnin Bowie aka haife ni nan kuma na girma. Iyaye na ‘yan asalin kasar Ghana ne. Mahaifiyata tayi aiki a fannin kula da hakori, tana da ‘yar sana’arta. Mahaifina kuma yana aiki a fannin da ya shafi na’urar komputa. Su sun koma birnin Greenbelt da zama, amma ni da kanwata da goggota da kawuna , da sauran dangina duka muna zama a Bowie. Shekara ta ishirin da biyar, nan aka haife ni, nan kuma na girma. Yanzu haka nine dan majalisar birnin Bowie mafi karancin shekaru.Nayi makaranta a Bowie kafin naje jami’a a Baltimore na kuma yi digiri na biyu a jami’ar America inda na sami digiri na biyu a fannin harkokin kasuwanci. Yanzu haka ina aiki da dan majalisa Steny Hoyer a matsayin manajan yakin neman zabensa.
Takarar zuwa Majalisar Bowie
Na dade ina tunanin abinda zan yi domin bada gudummuwa ga ci gaban wannan al’ummar sai nayi tunani cewa, mai yiwuwa farawa da zama memban wani kwamiti a majalisar shine matakin farko. Ya kuma kasance wadda take rike da kujerar kafin a zabe ni ta yi murabus daga matsayin, saboda haka naga wannan ne lokacin da ya dace. Na lura cewa, wannan yankin ne wurin kasuwancin Bowie. Munga babu wani abinda ake yi na inganta tattalin arziki. Kasuwar Bowie tana mutuwa. Babu wani ci gaba da ake samu a yankin. Kamar yadda na fada, babu wakilcin kwarai. Saboda haka na nemi cike wannan gurbin amma ban samu ba. Ta haka na tsaida shawarar cewa, idan ban samu matsayin ba, zan yi takarar kujerar a watan Nuwamba, abinda nayi ke nan.Mu biyar ne muka tsaya takara.
Yakin Neman Zabe
Ina jin sakon na ne jama’a suka gamsu da shi ya sa suka zabe ni. Mun lashe zabe da kuri’u hamsin da uku ne, ratar da muka bayar bata da yawa. Amma ina jin yadda muka gudanar da yakin neman zabenmu ne. mun yi kyakkyawan tsari, mun rika bugawa mutane waya muna nema su zabe mu. Mun kuma bi mutane gida gida. Mun rika kwankwasawa mutane kofa kusan kullum. Mun yi aiki tukuru. Ina jin abinda muke gaya masu ne. idan ka girma a nan , kayi aiki a nan, ka san abinda ya tsonewa mutane ido, ka san abinda ya dame mu da kuma san abinda suke so. Babu shakka mutane sun damu da ci gaban birnin, amma kuma suna son samun tabbacin cewa, wakilansu zasu yi abinda suke so. Abinda ya sa suka zabe ni ke nan.
Wani abu kuma da ya burge ni shine, lokacin da muke zaune muna kallon masu zuwa kada kuri’a, na lura cewa, da dama da muka tashi tare a birnin Bowie. Tsara na da yawa, sun fita kada kuri’a karon farko.
Abin Koyi A zaben Adrian
Ina cikin zuriyar farko a danginmu da aka Haifa a Amurka. Iyayena sun fito ne daga kasar Ghana. Abinda muke gani yana faruwa a wannan kasar yanzu, tun daga zaben shugaba Obama, da na ‘yan majalisar dokokin kasa. Idan ka tashi, kayi rayuwarka kana kiyaye doka da oda, zaka iya yin komi, musamman a birnin Bowie dake da matasa da dama kamar ni, dama ce ta cimma burin rayuwa a kasar nan. Iyayenmu sun zo kasar nan sun sadaukar da kansu domin bamu dama. Zamu iya amfani da wannan damar da suka bamu mu yi gaba, ko da kuwa iyayenmu ba ‘yan siyasa ba ne, ko kuma bamu fito daga iyalin da suke da kudin da zasu dauki nauyin yakin neman zabe da aka kashe makudan kudi ba. Idan kayi aiki sosai ka kuma kiyaye doka, zaka cimma burinka na rayuwa. Abinda muka yi ke nan, kuma ina jin sakon da muka aika ke nan da ya sa muka yi nasara.
Saurari Hirar cikin Sauti
Your browser doesn’t support HTML5