Yan CPC sun ce dan Arewa ne zai zamo dan takarar APC
Yan jam’iyyar CPC sun ce dan Arewa ne zai zamo dan takarar shugaban kasa na sabuwar jam’iyya da ake shirin kafa wa wato APC a zaben shugaban kasa na shekarar 2015. Wani jigo a jam’iyyar CPC kuma dan majalisar dokokin Najeriya Ahmed Mailantarki shi ya fada haka bayan da Ganaral Mohammed Buhari yace yana iya janyewa daga takarar idan har an samu wanda ya fishi.
Amma wani jigo a jam’iyyar ta CPC Awal Lalla yace ba tsayar da dan Arewa shi ne abun da ya fi mahimmanci ba. Yace muddin mutane basu dena karbar kudi ba domin su jefa kuri’a to ko gidan jiya za’a koma. Yace samun zabe mai inganci ya danganta ga al’umma wadanda zasu tsaya kan zaben mutane masu adalci, masu tsoron Allah da kuma masu kishin kasa.
Ita ko jam’iyyar PDP cewa ta yi hadewar sauran jam’iyyu wuri daya domin fuskantar PDP ba zai yi tasiri ba. Barayan Bauchi babban jami’I a fadar shugaba Jonathan yace wadanda suke neman kafa jam’iyyar APC ba don Allah ko kasar suke yi ba. Yace yawancinsu mutane ne da suka fice daga jam’iyyar PDP da wasu a fusace domin basu samu abun da suke so ba. Yace idan an tara duk kuri’un da suka samu a zaben da ya gabata basu sami kashin ashirin din kuri’un da shugaba Jonathan ya samu ba. Ta dalilin haka inji shi babu abun da zasu iya yi. Ya kara da cewa jam’iyyarsa ba zatu hana shugaba Jonathan tsayawa takara ba a zabe mai zuwa.

Your browser doesn’t support HTML5