Malam Yusuf Ibrahim shugaban wata kungiyar matasa musulmi da kirista a Najeriya yace bai gamsu da yadda 'yan siyasa ke anfani da matasa ba.
Yace na farko matasan yanzu a Najeriya basu ga anfaninsu a duniya ba gaba daya. Idan ana son a kashe mutane matasa ake sa kan gaba su aiwatar da ta'asar. Matasa ake anfani dasu a tayar da tarzoma.
Idan ana son cigaba matasa yakamata su kawo abun da zai taimaki kasa ta cigaba. Amma manyan 'yan siyasa basa anfani da matasa ta hanyar cigaban kasa sai dai idan ana son a yi barna.
To sai dai akwai wasu jihohi da suka ba matasa mukaman kwamishana. Misali ministan labarai na gwamnatin tarayya matashi ne. Duk da haka ana yin anfani da matasa a yi barna a gwamnati. Kamar maganar Boko Haram ta fara ne da matasan da aka yi anfani dasu a siyasa kana aka yi watsi dasu. Yanzu sun jefa kasar cikin wani mawuyacin hali da bai kamata kasar ta shiga ba.
Ya gargadi matasa cewa duk lokacin da 'yan siyasa suka nemesu su aikata wani mugun aiki su ce su kawo nasu 'ya'yan.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5