Dalilanmu Na Bai Wa Tompolo Kwangilar Biliyoyin Naira Ta Kare Bututun Mai - NNPC

Malam Mele Kyari

Wannan bayani na NNPC ba biyo bayan wasu rahotannin da ke nuna cewa kamfanin main a NNPC ya bai wa Tompolo din kwantaragin wuri na gugar wuri har Naira biliyan 48 ta kula da bututun mai.

Gwamnatin Najeriya ta yi wuf jiya Talata ta bayyana cewa ta yi daidai da ta bayar da kwangilar biliyoyin Naira ma tsohon jagoran kungiyar fafatukar kare yankin Naija Delta ta MEND, Government Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo,

Da ya ke bayani a zagaye na 49 na zaman saurare a fadar shugaban kasa da ke Abuja jiya Talata, Shugaban kamfanin NNPC, Alhaji Mele Kyari, ya ce an yanke wannan shawarar ce ala tilas saboda a lokacin Najeriya na bukatar wani kamfani mai zaman kansa wanda zai yi kwangilar kare rukunin bututan manta da ke sassan kasar saboda yawan sace man da ake yi. Malam Kyari ya ce wannan ba shi ne farau na bai wa daidaikun ‘yan Naija Delta kwangilolin kare bututun mai ba.

A cewar jaridar The Nation, kwangilar kula da bututan man ta kai Naira biliyan 48 a shekara, wato Naira bliyan hudu a wata guda.

Hedikwatar NNPC

Rahotanni na nuna cewa kungiyoyin ‘yan bindiga na yankin da dama na cike da fushi saboda rashin sa su cikin wannan kwangila mai tsoka, har sun shiga yin barazanar hana masu kwangilar kula da batutan man yin aikinsu.

Jiya Talata, Malam Kyari ya ce gwamnatin tarayya ba ta hulda kai tsaye da Tompolo. Ta na hulda ne da wani kamfani mai zaman kansa da shi Tompolon ke da hannu ciki.

Wasu bututan mai

“Jami’an tsaro na taka ta su rawar, kare bututan mai daga farko har zuwa karshe na bukatar kamfanoni masu zaman kansu da kuma masu zuwa da tsaki na cikin al’ummomin yankin da abin ya shafa,” a cewar Kyari.

A cewar Kyari an yanke shawarar ce saboda a cimma wasu manyan abubuwa uku: Ya ce na farko shi ne a tabbatar cewa jami’an tsaron gwamnati na nasu aikin. Mu na da sojojinmu na ruwa da kasa kuma su na aiki matuka wajen tsai da wannan matsalar. To amma yayin da ake wannan kuma ya kamata a tabbatar ya dore. Shi ya sa mu ka yanke shawarar cewa akwai bukatar ‘yan kwangila masu zaman kansu da za su iya kula da wuraren da kewaye da kuma iya hada kai da mu wajen hulda da mutanen cikin al’ummar.

“Ba mu da yanayin iya wannan, don haka sai mu ka bullo da wani tsari inda za a bayar da kwangilar yin hakan, kuma an zabi ‘yan kwangilar ne ta wajen bin wasu ka’idojin da aka gindaya ma mutanen da za su iya, saboda ba kowa zai iya yi ba. Kuma an dai ambaci sunan Tompolo ne kawai, amma da kamfanoni mu ka hulda. Ta yiwu ya na da hannu a kamfani, amma ba da Tompolo mu ke hulda ba, amma mun san ya na da hannu a kamfanin.”

Premium Times