Tallafin da aka kirkiro zai dinga ba wadanda suke cin gajiyar shirin Nera dubu biyar kowane wata.
Yace bisa da yin la'akari da irin halin da wadanda suka fi kowa talauci a kasar ya sa shugaban kasa ya fito da shirin tallafawa domin rage masu radadin kuncin rayuwa. Yace wanda ya riga ya tsufa babu abun da zai iya yi idan ba'a taimaka masa ba.
Dangane da inda aka samo kudin tallafin Alhaji Ibrahim yace a cikin kasafin kudin shekarar da ta gabata an yi tanadin nera biliyan dari biyar na tallafin.
Tsohon mataimakin gwamnan Babban Bankin Najeriya Dr. Obadiah Mailafiya yace shirin ya zo daidai lokacin da ya dace amma akwai damuwa daya. Yace a sa ido a tabbatar wadanda ya kamata su samu kudin suka samu, kada a yadda da cin hanci ko yin cuwa-cuwa da kudin.
Amma acewar Sabo Gashuwa bada tallafin ba shi ne mafita ba. Yana ganin kamata yayi a sa kudin cikin abubuwan da zasu farfado da tattalin arziki.
Jihohin Bauchi da Neja na cikin jihohin da za'a fara dasu. Misali a jihar Bauchi an fara shirin bada kudin ga mutane 10,800.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5