Rundunar ‘yan sandan jihar kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta kare kanta kan dalilin da ya sa ta dauki matakin haramta duk wani nau’in taro a daukacin jihar, inda ta ce matakin na da nasaba da kokarin ganin an tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
Rahotanni da dama sun ruwaito kakakin rundunar jihar DSP Abdullahi Haruna a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jihar a yau Asabar kan dalilin daukan wannan mataki.
A cewar rundunar ‘yan sandan, daukan matakin ya zama dole domin a kawar da duk wata barazana, ko daukan doka a hannu lura da irin barazanar da jihar fuskanta a ‘yan kwanakin nan.
Jaridun Najeriya da dama sun ruwaito rundunar ‘yan sanda a jihar ta Kano, tana gargadin cewa, duk wanda ya saba wannan doka, zai fuskanci fushin hukuma kuma za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.
Masu lura da al’umara, sun yi sharhin cewa, wannan mataki bai rasa nasaba da rikicin da ke tsakanin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da masarautar jihar.
Hukumar yaki da rashawa a jihar ta Kano tana tuhumar Sarki Muhammadu Sanusi II da ya yi bayani kan wasu kudade sama da biliyan uku da ake zargin an yi almubazzarancinsu wajen tafiyar da harkokin masarautar.
Dangantaka tsakanin shugabannin biyu, ta kara tsamari tun bayan zaben da aka kammala a farkon shekarar nan, inda wasu rahotanni ke cewa gwamnatin APC ta zargi Sarki Sanusi da nuna goyon baya ga bangaren ‘yan adawa na PDP.
Hakan ya sa Ganduje ya samar da sabbin masarautu hudu domin kassara tagomashin masarautar ta Kano, kamar yadda rahotanni ke nunawa.
Rahotanni da dama sun ruwaito cewa shugaba Muhammadu Buhari ya shiga tsakanin bangarorin biyu domin yin sulhu inda aka yi wani zama a jiya Juma’a.
Babu dai cikakken bayani kan yadda zaman ya kaya.