Takaddamar Rundunar Sojin Najeriya Da Kungiyar Amnesty

Tambarin kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International

“Akwai sahihan bayanai da ke nuna cewa reshen kungiyar da ke Najeriya, na da niyyar haifar da rudani a kasar.” In ji sanarwar rundunar sojin ta Najeriya, wacce ta wallafa a shafinta na Twitter.

Rundunar sojin Najeriya ta nemi kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International, ta rufe dukkanin ofisoshinta da ke kasar, muddin ba ta sauya abin da ta kwatanta a matsayin halin kungiyar "na kokarin haddasa husuma a kasar ba."

Wata sanarwa dauke da sa hannun Kakakin rundunar sojin ta Najeriya, Brig. Gen. Sani Usman Kukasheka, ta zargi kungiyar ta Amnesty da shiryawa wata makarkashiya da ka iya haifar da rudani a kasar.

“Akwai sahihan bayanai da ke nuna cewa reshen kungiyar da ke Najeriya, na da niyyar haifar da rudani a kasar.” In ji sanarwar rundunar sojin ta Najeriya, wacce aka wallafa a shafinta na Twitter.

Rundunar soji ta Najeriya ta kara da cewa “ta lura, kungiyar ta dukufa wajen kirkirar wasu karerayi na cewa jami’an tsaron kasar na take hakkin bil Adama, tare da zagayawa tana daukar nauyin kungiyoyi domin su fito su yi zanga zanga da kuma zargin shugabannin sojin Najeriya kan batutuwan da ba su da tushe.”

A cewar Kukasheka, kungiyar ta Amnesty na amfani da rikicin Boko Haram da na ‘yan Shi’a da kuma na makiyaya da kungiyoyi masu zaman kansu wajen cimma manufofinsu.

“Muddin idan kungiyar ba ta sauya salon yadda take al’amuranta ba, babu abin da ya rage mana illa mu ce su rufe ofishinsu da ke Najeriya.”

Sai dai kungiyar ta Amnesty International ta musanta wannan zargi, tana mai cewa dakarun na Najeriya sun sha jifansu da irin wadannan zarge-zarge.

"Ba ma so mu rika jayayya da su, saboda aikin da suke yi yana da muhimmanci, mun fi so su mayar da hankalinsu wajen kare darajar Najeriya." In ji Kakakin kungiyar a Najeriya Isa Sanusi.

Ya kara da cewa, "tun da suna da hujjoji, da kamata ya yi, tun suna da hujja, sai a gabatarwa mutane," saboda a cewar shi, ta haka ne za a iya ba su kunya.

Sanarwa ta sojin Najeriya, na zuwa ne a kuma daidai lokacin da kungiyar ta Amnesty ta fitar da wani rahoto wanda ya nuna cewa rikicin makiyaya da manoma a Najeriya, ya yi sanadin mutuwar mutane 3,600 tun daga shekarar 2016, mafi aksarinsu a wannan shekara.

Saurari hirar rahoton sanarwar sojin Najeriya daga Hassan Maina Kaina da kuma hirar Mahmud Lalo da Isa Sanusi na kungiyar Amnesty:

Your browser doesn’t support HTML5

Takaddamar Sojin Najeriya Da Kungiyar Amnesty - 4'55"