A hirar shi da Muryar Amurka, Ibrahim Shehu Adamu ya bayyana cewa, sun dauki lokaci suna gudanar da bincike inda suka yi amfani da kwarewa ta aikin jarida, suka yi hira da mutane a matakai da bangarori da dama da nufin fahimtar ayyukan ‘yan ta’adda da yadda ya shafi rayuwar al’umma ta yau da kullum, ta yadda za a iya daukar matakin dakile ayyukan ‘yan ta’addan da kuma shawo kan aukuwar matsalar nan gaba
Shugaban tashar Trust TV ya bayyana cewa, ministan watsa labarai na Najeriya Lai Mohammed na cikin masana da tashar ta yi hira da su a cikin shirin. Ya kuma bayyana cewa, sun yi hira da mutanen da ake cin zarafinsu saboda matsalar tsaro da ake fama da shi a wannan yankin, ya kuma ce an watsa shirin ne da nufin bada gudummuwa a yunkurin samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.
Mallam Ibrahim ya kara da cewa, “mu a matsayinmu ba mun yi ba ne domin mu sa matsalar ta ci gaba ko kuma mu daukaka wasu bisa wasu ba”. Ya bayyana cewa, za su ci gaba da yin abinda ya kamata da kiyaye dokokin yada labarai kamar yadda gwamnati ta gindaya.
A bayaninsa, shugaban hukumar ta NBC, Balarabe Shehu Illela ya ce sun ci tarar Trust TV ne domin abubuwan da ke cikin shirin na musamman da tashar ta watsa sun sabawa ka’idojin aikin jarida da ya bukaci mai irin wannan shirin ya yi la’akari da su. Ya yi misali da cewa, “dukan abinda za ka watsa ba za ka watsa shi domin ya kara ruruta wutar rikici ba, ba za ka yi shi ta yadda idan akwai yara a ciki ka nuna hotonsu ba, sannan akwai hirarraki da wadanda bai kamata ka yi hirarraki da su ba.” Ya ce duk wadannan abubuwa ne da ya kamata a yi la’akari da su.
Ya bayyana ma’aikatan tashar Trust TV a matsayin kwararru a fannin aikin jarida wadanda suka kuma san ka’idojin aikin sai dai a wannan karon sun yi kuskure.
Ya ce a matsayinsu na hukuma, ba su ki a sanar da al’umma abinda ya ke faruwa ba domin ainihin aikin dan jarida ke nan, sai dai “a matsayinmu na ‘yan jarida ko kuma wadanda su ke watsa labarai, muna da hakkin sanar da al’umma abinda yake faruwa, na biyu, muna da hakkin mu tabbatar da cewa, abinda mu ke fadan nan ba zai ruruta wutar rikici, ko ya yi zagon kasa ga ‘yancin Najeriya ko kuma zaman lafiyan Najeriya ba. Idan mu ka fahimci hakan zai faru a matsayinmu na hukuma ma isa ido dole mu takawa wadannan gidajen jarida birki domin nuna masu basu yi daidai ba.”
Ya kuma bayyana cewa banda Trust TV, Hukumar NBC ta ci wadansu gidajen watsa labarai tara, da su ka hada da kamfanin Multi Choice masu DSTV, da Star Times, da TSTV wadanda su ke da lasisin watsa shirye shirye a Najeriya, sabili da watsa wani shiri na musamman da tashar talabijin ta BBC ta shirya kan ayyukan ‘yan ta’dda a jihar Zamfara mai suna “Bandits Warlords of Zamfara.” Ya ce, akwai kuma wadansu gidajen jarida kamar BBC da suke nazarin matakan da za su dauka a kansu kasancewa tsarin aikinsu ya banbanta da wadanda su ke da lasisin aiki a Najeriya.
Kungiyar ‘yan jaridu ta kasa ta yi Allah wadai da wannan tara da Hukumar NBC ta ci tashar Trust TV da kuma matakan da take dauka kan kafofin watsa labarai.
A hirar shi da Muryar Amurka, mataimakin shugaban kungiyar ‘yan jaridu na kasa Alhassan Yahya ya ce ba kafofin watsa labarai kadai ba, amma duk dan Najeriya yana da ‘yancin fadin albarkacin baki kan abinda ya shafi rayuwarshi da ta ‘yan kasa. Ya ce wannan bai nuna kungiyar tana goyon bayan aikata ba daidai ba.
Alhassan Yahya yace idan har hukumar ta ga kamfanin watsa labaran bai yi daidai ba, abinda ya kamata ya yi na farko shine jawa kamfanin kunne da gargadi amma ba tara ba.
A nashi bayani, mai sharhi kan lamura Kwamred Isa Tijjani yace sun dade da dawowa da abinda ake kira da sunan yaki da ta’addanci a Najeriya, domin bisa ga cewarshi, wannan ya nuna kiri-kiri, an san su wanene su ke yi, an san abinda ya sa su ke yi an kuma san yadda za a yi a shawo kan ayyukan ta’addancin amma ba a sa. Ya yi misali da cewa, “babu dan Fulani da zai iya daukar bindiga yana yawo da shi, ko ya je ya kamo mutane ko ya harbi wani ya kashe ba tare da sanin Hardonsa ba, duk jejin nan duk hardon da ke kasar nan ya san abinda ke faruwa, amma gwamnatocin namu ba su so."
Bisa ga cewarsu, ko dai hukumomin ba su kudaden da su ke samu da sunan yaki da ta’addanci su yanke, ko kuma suna da wata alaka da ‘yan ta’addan. Yace “wannan abinda hukumar NBC ta yi tauna tsakuwa ce domin aya ta ji tsoro, dama ba a bukata a sani saboda haka don me ma kaje ka bincika.” Yace ya tabbata hukumar NBC ta zama karen farauta kawai domin bisa ga cewarshi, bai yi tsammani wannan matakin da hukumar ta dauka daga gareta ba ne. Ya ce yana yiwuwa umarni ne aka basu daga wani wuri domin wani yana ganin an yi ba daidai ba, amma ‘yan kasa suna da haki, suna da ‘yanci su san abinda ke faruwa.
Wadannan shirye shiryen na musamman din kan ayyukan ta’addanci a arewacin Najeriya da tashoshin BBC da Trust TV suka watsa ya ja hankalin al’umma sosai da ake ci gaba da yayatawa da kuma muhawara akai. Matakin da hukumar NBC ta dauka ya kuma kara jan hankalin wadanda basu kallli shirin ba da farko.
Kawo yanzu dai, kamfanonin da aka ci tarar suna nazarin martanin da zasu mayar kan tarar da hukumar NBC ta ci su.
A shekarar da ta gabata NBC ta ci kamfanin talabijin na Channels tara sabili da saba ka'idar aiki kamar yadda ta rubuta a wasikar da ta aikawa tashar.
Hukumar NBC ta kan wallafa ka'idoji da sharudan aikin kafofin yada labarai loto-loto a shafinta na twitter. Bayan cin tarar tashoshin na baya bayan nan, hukumar ta yi ta wallafa irin wadannan ka'idoji a shafinta na twitter.
Banda wadannan tashoshin da hukumar ta ci tara, shugaban hukumar ya bayyana cewa, suna nan suna nazarin matakan da za su dauka kan wadansu tashoshin kasashen waje da ya ce su ma an same su da laifin saba ka'idar aiki, sai dai ba a dauki mataki nan da nan kansu ba kasancewa ba su da lasisin aiki kai tsaye a Najeriya.
Ku Duba Wannan Ma Hukumar NBC Ta Samu Wasu Tashoshin Talabijin 3 Da Laifin Ruruta Zanga Zangar SARS.