Gwamnatin jihar Kaduna tace dalilin samun izinin kama shugabannin kungiyoyin matasan arewan Najeriya da suka baiwa 'yan kabilar Igbo wa'adi su bar arewacin kasar shi ne tabbatar da an bi doka da oda duk da janye wa'adin da suka yi.
Da yake karin haske gameda sanarwar da gwamnatin ta fitar akan kamo shugabannin, mai magana da yawun gwamnatin, Malam Samuel Aruwa yace ko menene ma dole doka tayi aikinta.
Yana mai cewa daga lokacin da mutum ya karya doka wajibi ne a nemoshi ya amsa laifinsa.
Akan cewa tunda suka janye wa'adin kamosu yanzu tamkar maida hannun agogo baya ne sai Aruwa yace idan mutum ya yi abun da ya tadawa jama'a hankali ko ya dawo ya janye ya riga ya sabawa doka dole a tuhumeshi. Yace ana maganar doka ce tare da kare rayukan mutane da dukiyoyinsu.
Mr Aruwa ya lissafa tsarin dokokin da matasan suka sabawa da yanzu ya zama wajibi su amsa.
Amma Alhaji Abdulaziz shugaban matasan da ake son a kama yace yana da ta cewa. Yana cewa sun kalli abun ta bangarori biyu ne. Injishi, idan kotu ta bada izinin a kama mutum 'yansanda zata ba su kama mutum ba gwamna ba. Abu na biyu gwamnan da mutanensa na son kawo tashin hankali ne a arewa.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5