Dalilin Da Ya Sa China Tafi Sauran Kasashe Mamaye Afirka

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum

A lokacin da Amurka da China da kasashen Yamma ke fafatawa a gasar wa yafi kusanci da kasashen Afirka, shugaban kasar Nijar ya danganta nasarar da China ke samu a Afirka da rashin tsoro.

Tasiri da zuba hannun jari da kasar China ta yi a nahiyar Afirka ya farbar da kawayen hamayyarta musamman Amurka da sauran kasashen Yammacin duniya, inda yanzu ke zaman tamkar gasa ce tsakaninsu bisa hasashen habakar jama’a da harkokin kasuwanci da ake sa ran samu nan da shekaru masu zuwa.

Yayin halartar taron kolin Amurka da Afirka, shugaban kasar Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum, ya bayyanawa sashen Hausa cewa rashin tsoron zuwa kasashen Afirka tun farko daga kamfanonin kasar China, sabanin na kasashen Yamma, shine ya habaka dangantakar China da Afirka a halin yanzu.

Duk da, idan an kwatanta da kasar Amurka, kasar China ita ce ta mallaki yawancin kamfanonin kasarta.

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum da shugaban sashen Hausa Aliyu Mustpha

A tattaunawarsu da shugaban sashen Hausa Aliyu Mustapha Sokoto, shugaba Bazoum, ya kare zargin dogara ga turawan Faransa don samin tsaron cikin gida, inda ya kwatanta Nijar da kasar Mali dake cikin wani hali, biyo bayan kin amincewa da taimakon sojoji daga Yamma, maimakon haka suka dauko sojojin haya na kasar Rasha.

A lokacin da shugaba Joe Biden zai yi magana da shugabannin Afirka a birnin Washington ranar Laraba, ana sa ran jin goyon bayan dimokuradiyya, da ci gaban tattalin arziki da kuma sabbin alkawurran kudi na yankin da a shekarun baya-bayan nan ya samu koma baya ga wasu muhimman abubuwan da Amurka ta sa gaba.

Amma za a sami wani sako, mai yiwuwa ba a fadi ba: Amurka ta kasance abokiyar abokiyar Afirka fiye da China.

Yanzu haka dai Tawagogin kasashe 49 da kungiyar Tarayyar Afirka, da suka hada da shugabannin kasashen Afirka 45, na halartar taron na kwanaki uku, wanda aka fara a ranar Talata, irinsa na farko tun shekara ta 2014, inda Washington za ta kuma bayyana goyon bayanta ga samar da abinci da sauyin yanayi.

A ziyarar da shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum, ya amsa tambayoyi kama daga tattalin arziki da tsaro da kiwon lafiya da dai sauran muhimman batutuwa.

Domin Karin bayani saurari hirar shugaban sashen Hausa da shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum.

Your browser doesn’t support HTML5

Dalilin Da Ya Sa China Tafi Sauran Kasashe Mamaye Afirka - 13'24"