Dalilin Da Ya Sa APC Ta Dakatar Da Okorocha, Amosun

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha

Kwamitin zartarwa na Jam’iyyar All Progressive Congress (APC) ya dakatar da gwamnan jihar Imo da takwaran aikinsa na Ogun, Ibikunle Amosun daga jam’iyyar.

Rahotanni sun nuna cewa, an yanke shawarar dakatar da gwamnonin biyu a taron kwamitin gudanarwar jam’iyyar, saboda ana zarginsu da yi wa jam’iyyar ta APC zagon kasa.

“Rashin tarbiya da rashin nuna biyayya, a lokacin da muka je yakin neman zabe, (Ibekunle) ya sa yara suka rika jifa, sannan yana ta kamfe domin a zabi dan takarar gwamnan wata jam’iyya.” Inji Sakataren walwala a jam’iyyar ta APC na kasa Alhaji Ibrahim Kabiru Masari.

Sai dai wani na hannun daman gwamnan Amason Ibekunle mai suna Abdullahi Suleman, ya ce, “tsakani da Allah ni gaskiya ina ganin babu hannunsa a ciki, kuma shi gwamna yana tare da Baba Buhari.”

Shi ma gwamnan jihar Imo Okorocha, an zarge shi ne da laifin yi wa jam’iyya zagon kasa, inda yake goyon bayan wani dan takarar gwamna da ba na APC ba.

“An ma yi jinkiri wajen dakatar da shi, ya kamata tun shekara daya da ta gabata a dakatar da shi, Rochas ba amintaccen dan jam’iyya ba ne.”Inji Dr. Ikechi, wanda jigo ne a jam’iyyar ta APC.

Sai dai a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, Sakataren yada labaran gwamna Okorocha, Sam Uwuemeodo, ya zargi shugaban jam’iyyar ta APC, Adams Oshiomole da kokarin ruguza jam’iyyar ta APC.

Ya kara da cewa, shugaban jam’iyyar ta APC, yana ta kokarin ya ga an muzgunawa yankin kudu amso gabashin Najeriya (da al’umar Igbo suke.)

Saurarin cikakkun rahotannin da Alphonsus da Hassan suka turo mana, wadanda muka hade hancinsu:

Your browser doesn’t support HTML5

Dalilin Da Ya Sa APC Ta Dakatar Da Okorocha, Amosun - 4'35"