Dalilin Amurka Na Hana Shiga Da Manyan Na’urori Cikin Wasu Jiragen Da Suka Nufi Kasar

Mutum-mutumin da ake kira Statue of Liberty a Amurka, wanda wuri ne da Amurka take tunkaho da shi.

Hukumar dake kula da tsaro a fannin sufuri a Amurka, ta fitar da wani umurnin gaggawa wanda zai hana wasu filayen jirage bai wa fasinojinsu damar shiga da manyan na'urori cikin jiragen da suka nufi Amurkar.

A yau Talata hukumar ta fitar da wannan umurni wanda ya shafi filayen tashin jirage goma daga yankin, wadanda sukan shiga Amurka ba tare da sun yada zango a wata kasa ba.

Hukumar ta ce ba wai akwai wata barazana ba ce karara, sai dai domin an lura cewa ‘yan tadda na ci gaba da yunkurin kaikaitar jiragen fasinja wajen kai hare-hare.

Wannan umurni zai tilastawa fasinjoji su saka manyan na’urorin da suka fi girman wayar salula su ajiye su a sashen ajiye kaya.

Bayanai sun yi nuni da cewa ba a zabi hana shiga da wayar salula ba ne saboda wasu dalilai na gudanar da aiki.

Filayen tashin jiragen da wannan umurni zai shafa sun hada da Queen Alia da na Cairo dake Masar da Ataturk na Turkiyya, da na King Abdulaziz da na King Khalid da na Kuwaiti da sauransu.