‘Yan sandan kasar Sudan sun yi arangama da dalibai yau Lahadi yayinda wata zanga zangar kin jinin gwamnati ta barke a Khartoum babban birnin kasar. Daruruwan dalibai suka shiga sahun masu zanga zanga suna raira taken dake kushewa tsadar rayuwa da gwamnati da kuma shugaba Omar al-Bashiri. An yi zanga zanga a wurare akalla uku, da suka haka da tsakiyar birnin Khartoum da kuma wadansu jami’oi biyu. Shaidu sun ce a daya daga cikin makarantun, dalibai sun rika jifan ‘yan sanda da duwatsu wadanda suka maida martani da duka da kulake. Hukumomi sun ce an kama mutane biyar. Daliban sun amsa kiran da aka yi ne ta hanyar sadarwar internet na yin zanga zangar ruwan sanyi ta kin jinin gwamnati. Daliban sun ce suna koyi ne da zanga zangar da aka yi a kasar Tunisiya da ta hambare gwamnatin shugaban kasar da kuma wadda ake yi a halin yanzu a kasar Masar.
‘Yan sandan kasar Sudan sun yi arangama da dalibai yau Lahadi yayinda wata zanga zangar kin jinin gwamnati