Ranar Laraba ne wasu ‘yan bindiga suka afka wa makarantar kimiyya ta gwamnati dake garin Kagara a jihar Neja, suka kwashe dalibai suka yi awon gaba da su. Sai dai wasu daga cikin daliban sun sami tsallake rijiya da baya, ta hanyar gudu cikin daji.
Daya daga cikin daliban da suka sami nasarar kubucewa daga hannun ‘yan bindigar, ya bayyana wa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa, ‘yan bindigar sun gargade su da cewa duk wadanda suka gudu zasu harbe su, amma duk da haka wasu sun samu sun gudu.
Haka kuma dalibin ya ce ‘yan bindigar sun kamo wasu da suka yi yunkurin gudu, suka hada rigunan mutane biyu su daure.
Shi ma wani dalibin da ya kubuta ya fada wa Sashen Hausa cewa, lokacin da suka fahimci abin da ke faruwa a makarantar, mafi yawan dalibai sun ruga cikin daji, inda suka yi ta tafiya mai tsawo don tabbatar da cewa sun yi wa ‘yan bindigar nisa, kafin su samu wata katuwar itaciya su ka kwanta har zuwa wayewar gari.
Alhaji Abdulkarim, na daya daga cikin iyayen yaran da ‘ya ‘yansa biyu suka kubuce daga hannun ‘yan bindigar, “Daya daga cikin ‘ya‘ya na ya kira ni ta waya ya ce, Baba kasan mun kwana cikin tashin hankali, domin karfe ‘daya na dare wasu suka shiga da bindigogi da kakin soja, suka rika tashinsu da bulala.”
Tuni dai gwamnatin Najeriya ta sha alwashin ganin ta kwato yaran dake hannun ‘yan bindigar, ta bakin Ministan ‘yan sanda, Alhaji Muhammad Maigari Dingyadi, lokacin da suka ziyarci jihar Neja sakamon wannan al’amari.
Ya kuma tabbatar da cewa yanzu haka shugabannin tsaron Najeriya su na aiki don ganin an sami kubutar da dukkan wadanda ‘yan bindiga suka kama domin mayar da su ga iyalansu.
Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, wanda ya ziyarci makarantar Kagara ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da tayar da hankali.
Domin cikakken rahoton saurari Mustapha Nasiru Batsari ta sauti.
Your browser doesn’t support HTML5
Karin bayani akan: jihar Neja, Kagara, Abubakar Sani Bello, Nigeria, da Najeriya.