Jadawalin da hukumar ta NECO ta fitar ya nuna daga yau zuwa litinin ta mako gobe, jimlar darrusa 30 ne daliban zasu rubuta jarabawar su, wadanda suka hada da darasin tattalin gida da na koyon dabarun girke-girke da na koyon aikin kafinta da dai sauransu.
Sai dai daliban da suke kammala karatun sakandare a makarantun gwamnatin Kano ba za su sami zarafin rubuwa wannan jarabawa ba, saboda rashin biyan kudaden jarabawa ga hukumar NECO.
Rahotanni sun ce kimanin naira miliyan dubu ne hukumar ta NECO ke bin gwamnati bashi, a don haka sai ta tsame daliban Kano wadanda ke karatu a makarantun gwamnati daga jerin masu rubuta jarabawar ta yau, al’amarin da ya jefa daliban da iyayen su cikin rudani.
Ku Duba Wannan Ma An Yaba Da Sakamakon Jarabawan SakandareSai dai kwamishinan labaru na Kano Mohammed Garba yace adadin da hukumar ta NECO ke bin gwamnati bai kai haka, kuma dama akwai alkawarin tsarin biyan kudaden tsakanin gwamnati da hukumar.
Kazalika kwamishinan labarin na gwamnatin Kano ya baiwa dalibai da iyayen su tabbacin cewa, gwamnati na yin duk mai yuwuwa wajen ganin ta biya
Baya ga hukumar NECO, ita ma hukumar BABTEB dake shirya jarabawar daliban da suka kammala makarantun arabiyya da dangogin sun sami irin wannan takaddama da gwamnatin Kano a bara, inda hukumar ta rike sakamakon jarabawar daliban Kano kafin daga bisani aka sasanta.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5