Dalibai da dama daga arewacin Borno rikicin Boko Haram ya daidaita. Rikicin ya katse karatunsu ya jefasu da iyayensu cikin wani halin rudani sakamakon kwace garinsu da 'yan ta'adan suka yi. Lamarin ya hanasu kammala karatunsu a garuruwansu na asali
Da taimakon Allah da na wani mai jin kai yau daliban suna daukan daratsi da nufin kammala karatunsu saboda su samu daman yin jarabawar WAEC da NECO. Daliban su kusan dari biyar sun samu taimakon ne daga Alhaji Abubakar Kyari wanda ya dauki nauyin kammala karatun nasu da kuma wasu malamai matasa daga arewacin Bornon. Su malaman suna koyas da daliban kyauta ne.
Daliban du suka hada da 'yan mata da samari suna daukan daratsi ne a birnin Maiduguri. Da Muryar Amurka ta tambayi Alhaji Abubakar Kyari dalilin daukan nauyin daliban sai ya ce dama can shi yana kukan rashin ilimi a jiharsu. Yace jiharsa da ma arewacin Najeriya suna baya akan harkar ilimi. Bugu da kari sai ga masifar Boko Haram da ta addabi yankin kuma idan ba'a tashi tsaye ba to za'a yi asara da komawa baya.
Alhaji Kyari yace koda dalibai dari hudu ko biyar aka samu aka tallafawa to cigaba ne. Yace idan suka nade hannuwansu basu yi komi ba asara ce garesu. Ya kira jama'a su tashi tsaye su taimaka.
Shirin da Alhaji Kyari ya yiwa daliban ya hada da dafa masu abinci kyauta a wurin da suke daukan daratsi. Ya saya masu littafan karatu tare da motoci da suke jigilarsu daga inda suke zaune zuwa wurin da suke daukan daratsi. Daliban suna zaune ne a sansanonin 'yan gudun hijira dake cikin birnin Maiduguri.
Ibrahim Hassan shi ne shugaban kungiyar matasan dake ba daliban daratsi yace sun fi hamsin da suka dauki nauyin koyasda daliban domin samun magada ko bayan ransu. Suna koyaswa kyauta ne ba da biyansu ko kwandala ba.
Ga karin bayani daga Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5