Dalibai Basu Iya Biyan Kudaden Jami'oi Masu Zaman Kansu

Bayero University

Masana harkokin ilimi na ci gaba da bayyana hanyoyi daya kamata hukumomi a Najeriya su bi domin warware kalubalan da bangaren ilimi ke fuskanta tun daga matakin karamar sakandare zuwa Jami’a.

A makalar da ya gabatar a taron shekara shekara na kungiyar tsofaffin daliban Kwalegin Gwamnati, dake garin birini kudu,dake jihar Jigawa,kwararre kan ilimi a Najeriya, Dr. Ayuba Tanko Abubakar, yace alkaluma sun nuna cewa kashi goma cikin dari ne kawai na daliban da suka cancanta suka sami shiga Jami’a, a shekarar da ta gabata.

Ra’ayi dai ya banbanta tsakanin masu nazari a fagen ilimi a Najeriya, game da matakin kara yawan jami’oi, a Najeriya, ko kuma fadada wadanda ake dasu da nufin baiwa kowane dalibi ‘yancin samun gurbin karatu a jami’a.

Shugaban kungiyar shuwagabanin Jami’oin, Afirka, ta yamma, kuma shugaban Jami’an, jihar Jigawa, Farfesa Abdullahi Yusuf Ribado, yace a Najeriya, yanzu akwai Jami’oi, kusan dari da hamsin da biyu (152) masu zaman kansu kusa sittin da takwas (68) amma daliban da Jami’oin, suke dauka bai kai goma cikin dari ba na wadanda ke neman shiga jami’oi, ba.

Duk da yake akwai gurbi amma daliban bazasu iya biyan kudin makarantar ba tilas su nemi na Gwamnati, saboda haka fadada Jami’oi, yana da amfani.

Your browser doesn’t support HTML5

Dalibai Basu Iya Biyan Kudaden Jami'oi Masu Zaman Kansu- 3'29"