Dalibai 42 Sun Samu Horon Sarrafa Harshe da Tsarin Magana A Adamawa

Bikin saukar dalibai da suka yi karatun fasahar sankira ta zamani

Cibiyar Konkol Silver Tongue ta farko a arewacin Najeriya dake Yola fadar jihar Adamawa ta yaye dalibai arba’in da biyu da suka sami horo kan fasahar sarrafa harshe, zubi da tsarin magana na gabatar da shirye-shirye a manyan tarurruka, bukukuwa da walima.

Fasahar wadda kamar ta sana’ar sankira a al’adar Hausa ce yanzu haka sana’a ce da ke bunkasa a sauran sassan Najeriya. Ta zama wata hanyar samarwa dimbin jama’a sanar dogaro da kai dalili ma da ya sa aka kafa cibyar ke nan inji shugaban ta Dr. Abba Tahir na jami’ar Amurka a Najeriya dake Yola.

Dr. Tahir yace bayaga koyar da fasahar sarrafa harshe, zubi da tsarin magana cibyar na koyawa ‘yan jarida karin harshe da yadda ake rubuta jawabai na shugabanni da manyan jami’an gwamnati.

Tsohon janar manajan gidan telabijan na tarayya Cif Timawus Mathias ya fada a hirar da Muryar Amurka ta yi da shi cewa musamman matasa su zasu fi anfana da horon da suka samu saboda sana’a ce da zata samar masu da wata kafa ta yin dogaro da kai.

Malama Rabi Usman da Abdurahaman Abba wasu daga cikin dalibai da cibiyar ta yaye wadanda sun yi bayanin abubuwan da suka anfana da suka hada da kyautata mu’amalarsu da jama’a, habaka sana’arsu da kuma samar masu da wata kafa da yin dogaro da ita tamkar sana’a.

Daga cikin dalibai da cibiyar Konkol Silver Tongue ta yaya akawai ‘yan jaridu, jami’an tsaro, ma’aikatan gwamnati, lauyoyi da ‘yan kasuwa.

Saurari Karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.

Your browser doesn’t support HTML5

Dalibai 42 Sun Samu Horon Sarrafa Harshe da Tsarin Magana A Adamawa - 3' 04"