Dakarun 'yan tawaye da sojojin Mali na gwabza fada a Gao

  • Ibrahim Garba

Bamako, babban birnin kasar Mali

Shaidu sun gaya wa Muryar Amurka cewa dakarun tawaye

Shaidu sun gaya wa Muryar Amurka cewa dakarun tawaye na gwabazawa da sojojin Mali a birnin Gao na arewacin Mali. Ana iya jin mayan kararrakin barin wuta.

Wani wakilin Muryar Amurka da ke wurin ya ce akwai bayanan shaidun gani da ido da ke nuna cewa dakarun ‘yan tawaye cikin motacinsu sun kutsa cikin garin na Gao, dauke da tutocin Azawab na kasar da su ke niyyar kafawa.

Kara dannawar da dakarun tawayen su ka yi zuwa cikin Gao ya faru ne kwana guda bayan da ‘yan awaren su ka kwace garin Kidal.

‘Yan tawayen Asbinawan sun fara yakin sunkurun ne a cikin Janairu.

A makon jiya dai sojoji a Bamako, babban birnin kasar Mali, sun hambarar da gwamnatin da aka zaba a dimokaradiyyance. Sojojin sun ce suna bakin ciki ne da gazawar gwamnati game boren na Asbinawa a arewacin kasar.