Dakarun Turkiya Sun Kutsa Cikin Iraqi

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan,

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan,

A karon farko tun shekarar 2011 dakarun Turkiya sun kutsa cikin Iraqi suna farautar 'yan tawayen kurdawa da suka kai ma kasar hari.

Dakarun Turkiya dake yaki a doron kasa, sun kutsa arewacin Iraq jiya Talata karon farko tun shekara ta dubu biyu da goma sha daya, suka gudanar da abinda jami’ai suka bayyana a matsayin wani shirin farautar ‘yan tawaye Kurdawa da suka kaiwa sojoji da ‘yan sandan Turkiya hari.

Ba tare da karin bayani ba, wani jami’in gwamnatin Turkiya yace dakarun sun shiga yankin ne yayinda suke farautar haramtaciyar kungiyar Kurdistan Workers’ Party ko kuma PKK a takaice.

Mayakan saman kasar Turkiya sun kai hari ta sararin sama jiya talata da safe kan sansannan kungiyar PKK dake Iraq. Kamfanin dillancin labaran Anadolu yace sama da jiragen saman Turkiya 50 suka kai summanen na tsawon sa’oi shida, suka kashe ‘yan tawaye 40.

Wani harin bom da aka kai gefen hanya jiya kuma ya kashe a kalla ‘yan sanda 14 a lardin Igdir dake gabashin Turkiya.

Jakadan Birtaniya a Turkiya ya yi kira da a kawo karshen tashin hankali da ya kira marar ma’ana, ya kuma yiwa iyalan sojoji da ‘yan sandan da aka kashe kwanan nan jaje.