Dakarun Saudiyya da Na Kawayenta Sun Kai Harin Sama Kan Kasar Yamal

Sarkin Saudiyya Sarki Salman

A wani matakin da ya zama tamkar maida martani ne, kasar Saudiyya da kawayenta sun kaddamar da hari ta sama kan kasar Yamal inda 'yan tawaye masu samun goyon bayan Iran suka harba makami mai linzami zuwa kasar ta Saudiyyan

Dakarun Saudiyya da na kawayenta sun kaddamar da wani hari ta sama a kasar Yamal, inda Saudiyyar ke jagorantar rundunar hadin gwiwar sojoji domin yakar ‘yan tawayen Houthi da Iran ke marawa baya tun watan Maris din shekarar 2015.

Gidan Talibijin na Alhurra ya rawaito cewa an kai hare-haren ta sama ne jiya Lahadi akan ginin ma’aikatar tsaro da ma’aikatar gudanar ayyukan cikin gida da kuma sauran wasu gurare a birnin Sana’a.

Wadannan hare-haren dai na zuwa ne kwana guda bayan da Sojojin Saudiyya suka ce sun kakkabo wani makami mai linzami da aka harbo daga Yamal, wanda aka auna filin saukar jiragen sama na King Khalid dake a Arewa maso gabashin Riyadh.