Dakarun Najeriya Sun Kashe Mayakan sakan Nija Delta 114 A Legas Da Ogun.

Tankunan yaki na sojojin Najeriya

Darektan yada labarai na mayakan Najeriya Birgediya Janar Rabe Nasir ne ya bayyana haka.

A Najeriya rundunar mayakan kasa dana sama da na ruwa sun kai farmaki na hadin guiwa a jihohin Legas da Ogun, wanda ya halaka akalla mayakan sakai 114 da raunata wasu masu yawa.

Wannan ya biyo bayan farmakin da dakarun suka kai kan sansanonin mayakan sakan a wadannan jihohi dake kudu maso yammacin kasar. Birgediya janar Rabe Nasir, wanda shine darekatan yada labarai na mayakan kasar, yace bayanai daga jami'an leken asiri na mayakan kasar sun nuna cewa mayakan sakai daga yankin Nija Delta suna buya a dazukan dake ciki ko kan gabar ruwa.

A baya bayan nan dai mayakan sakan sun zafafa kai hare hare kan bututun mai da wasu muradun mai a yankin Nija Deltan mai arzikin mai, kuma sunyi barzanar zasu yi kara yin barna kan kadarorin mai dake yankin.

A hira da yayi da MA, Birgediya Janar Abubakar yace matakin sojin wani bangare ne na tabbatar da diyaucin kasar. Yace farmakin zai hana mayakan 'yancin walwala, tareda lalata sansanonisu domin hana su wuri da zasu shirya kai wasu hare hare.

Wannan ya biyo bayan bayanai da 'Yan kasar suka baiwa jami'an tsaro cewa mayakan sakan suna amfani da gabar ruwa da dazukan dake jihohin na Ogun da Lagos domin su sake yin damara domin komawa yankin Nija Delta inda zasu kai karin hare hare kan kadarorin mai.