Dakarun kasar Siriya sun fara kai farmaki a wani birnin dake arewacin kasar.

Masu zanga zanga a kasar Siriya

Tashar talabijin ta kasar Syria tace rundunar sojin kasar ta fara aiki yau Jumma’a na “maido da tsaro” a birnin Jisr al-Shughbour dake arewacin kasar kusa da kan iyakar Turkiya.

Tashar talabijin ta kasar Syria tace rundunar sojin kasar ta fara aiki yau Jumma’a na “maido da tsaro” a birnin Jisr al-Shughbour dake arewacin kasar kusa da kan iyakar Turkiya. Bisa ga cewar tashar talabijin din, sojojin sun yunkura wajen kwato ikon birnin ne bisa bukatar da mazauna garin suka gabatar da rahoton yace sun roki sojojin su kama “yan banga dake dauke da makamai” wadanda gwamnati tace saun kashe jami’an tsaro 120 farkon makon nan. Tun farko mazauna birnin sun ce sojojin dake biyayya da gwamnati sun kaiwa dakarun da suka bijire ko kuma wadanda suka ki bude wuta kan farin kaya hari, yayin zanga zagar kin jinin gwamnatin da aka gudanar makon jiya. Shaidu sun ce dakaru da tankoki sun yada zango bayan birnin jiya Alhamis. Sai dai ‘yan gwaggwarmaya sun ce akasarin mazauna birnin jist al-Shughour dubu hamsin sun kauracewa birnin, da dama zuwa Turkiya kafin a fara kai sumamen. A halin da ake ciki kuma, ‘yan gwaggwarmayar kare damokaradiya sun yi kira da a gudanar da wata sabuwar zanga zaga yau jumma’a ta nuna kin jinin gwamnatin Mr. al-Assad. Kungiyoyin kare hakin bil’adaman sun ce an kashe kimanin mutane dubu daya da dari daya yayinda gwamnatin kasar Syria tayi amfani da karfi wajen murkushe masu zanga zangar da aka fara a watan Maris yayinda aka kama kimanin mutane dubu goma. Kungiyar agaji ta Red Cross dake birnin Geneva ta yi kira ga kasar Sham ta bada izinin isa ga wadanda suka ji raunuka ko kuma wadanda ake tsare da su. Yau jumma’an ne har wa yau, Firai Ministan Turkiya Tayyip Erdogan yace ya yi magana da shugaban kasar Syria a cikin ‘yan kwanakin da suka shige ya bukace shi da ya yiwa gwamnatinsa garambawul. Mr. Erdogan ya bayyana cewa ba za a lamunci murkushe masu zanga zanga da gwamnatin ke yi ba, ya kuma bayyana yadda ake wulakanta jikunan matan da jami’an tsaro suka kashe a matsayin mugun laifi. Sakataren tsaron Amurka Robert Gates ya fada a birnin Brussels cewa, “yankan rago” da ake yiwa mutanen da basu ci ba basu sha ba abin damuwa ne ga kowa. Jiya alhamis ministan harkokin kasashen ketare na kasar Turkiya Ahmet Davutoglu yace kimanin Siriyawa dubu biyu da dari biyar ne suka shiga kasar, ya kuma ce Turkiya bata da niyyar rufe kan iyakokinta.