Dakarun Kamaru, 'Yan aware Na Zargin Juna Da Kashe Farar Hula 35

Dakarun Kamaru a yankin da ke amfani da Ingilishi a ranar 9 ga watan Janairu, 2020. (M. Kindzeka/VOA)

Akalla farar hula 35 ne rahotannin suka nuna sun rasa rayukansu sannan an kona gidaje 40 cikin kasa da mako guda a yankin Kamaru da ke amfani da harshen Ingilishi.

Lamarin ya biyo bayan wata mummunar arangama da aka yi tsakanin dakarun kasar da mayakan 'yan aware da ke fafutukar kafa kasar Ambazonia.

Gwamnati da mayakan ‘yan awaren na zargin juna da alhakin mutuwar fararen hular, ciki har da yara kanana da suka makale a cikin gidajensu da aka kona.

Bruno Ngeh mai shekara 38, ya ce ‘yar uwar matarsa da iyalanta tara duk sun mutu a hare-haren da aka kai Ngarr-buh; daya daga cikin kauyukan da lamarin ya rutsa da su.

"Wadannan mutanen sun tsere ne zuwa kauyen na Ngarr-buh, suna tunanin cewa sun gujewa wannan rikici, amma sai ga shi dakarun da ya kamata su kare lafiyarsu, sun bi su har gida suna bacci sun kashe su.” Inji Ngeh.

Sai dai kwamandan tsaron kasar, Laftanar Janar Rene Claude Meka, yayin da yake wani jawabi a kafar yada labaran CRTV, ya musanta hannun dakarunsa a wannan aika-aika

"Ya kamata kowa yan san cewa, dakarun kasar sun je ne su kare Kamaru da al’umarta daga hare-haren ‘yan ta’adda, a wannan yanayi da muke ciki, muna bukatar hadin kan al’umar Kamaru.” Meka ya ce.