Dakarun Janar Haftar Sun Shiga Filin Tashin Jiragen Birnin Tripoli

Wannan wani hoton ne da ke nuna dakarun da ke goyon bayan Janar Haftar a kudancin Libya

Babu dai wasu rahotanni da suka nuna cewa dakarun sun fuskanci turjiya wajen shiga filin tashin jiragen.

Firai Ministan Libya da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, Fayez Sarraj, ya ce dakarun gwamnatinsa na cikin shirin tunkarar mayakan da ke goyon bayan kwamandan sojojin gabashin kasar ta Libya, Janar Khalifa Haftar, wadanda ga dukkan alamu sun samu galabar karbe ikon wajen babban birnin Tripoli.

Firai minister Sarraj, ya kwatanta wannan lamari a matsayin juyin mulki.

Kafafen talbijin din kasashen larabawa, sun nuna wani bidiyo da ke nuna yadda dakarun Janar Haftar suke kutsa kai cikin filin tashin jirage na Tripoli wanda yanzu ba a amfani da shi.

Babu dai wasu rahotanni da suka nuna dakarun sun fuskanci turjiya wajen shiga filin tashin jiragen.

Kafafen yada labarai na kasashen larabawa, sun nuna wasu mazauna yankin babban birnin suna ta murna a lokacin da dakarun suke kutsa kai cikin filin tashin jiragen.

Kafar talbijin din kasar Saudiyya na Al Arabiya, ya ce, dakarun Haftar, sun shiga Lardin da ake kira Khalat al-Fargan da ke birnin na Tripoli.