Yau Litinin dakarun kasar Iraqi suka kwace ikon wata gada mai muhimmanci a birnin Mosul, a ci gaba da kokarin kakkabe mayakan IS daga gabashin birnin.
WASHINGTON DC —
Jami’ai sunce dakarun gwamnati sun kawace gadar da ake kira ”Gada ta hudu” ko kuma “Gadar kudanci” data ratsa tekun Tigris. An lalata galibin gadojin dake Mosul sakamakon yaki da aka yi ta gwabzawa a birnin. Bude gadar zai ba rundunar soji damar tura dakaru da kuma dakon kayan da ake bukata.
Yayinda fada yake kara zafi a yammacin Mosul, ana fargaba kan makomar farin kaya a birnin. Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ta bayyana yanayin da farin kaya suke ciki da tace suna fuskantar karancin abinci, da makamashi da kuma magunguna.
Farinkaya da dama sun kaura zuwa yammacin Mosul bayanda mayakan suka kwace ikon gabashin birnin a watan Nuwamban bara