Dakarun Gwamnatin Syria Sun Kai Hari Kan 'Yan Tawaye a Birnin Damascus

Wurin da dakarun gwamnatin Syria da 'yan tawaye suka gwabza fada a birinin Damascus

Dakarun Syria sun mayar da martani a kan ‘yan tawaye a babban birnin kasar Damascus, kwana guda a bayan da mayakan yan adawan suka kai farmaki a kan wasu unguwanni dake karkashin ikon gwamnati a arewa maso gabashin birnin.

Dakarun Syria sun mayar da martani a kan ‘yan tawaye a babban birnin kasar Damascus, kwana guda a bayan da mayakan yan adawan suka kai farmaki a kan wasu unguwanni dake karkashin ikon gwamnati a arewa maso gabashin birnin.

Shaidu sun ce sun ga jiragen yaki na dakarun gwamnati suna kai hare-hare a Damascus, sai dai ba a tabbatar da ko masu tuka jiragen sojojin gwamnati ne ko kuma na kawarta Rasha, wadanda suke marawa shugaba Bashar al-Assad baya.

Fadan na yau Litinin ya hada ne da unguwar Jobar inda mayakan yan adawan suka kwace gine gine da dama a jiya Lahadi a wani farmaki da suka kai, wanda ya faro da tada wasu bamabamai a mota da kuma kai hare haren kunar bakin wake.

A cikin shekara guda da ta shige, ‘yan tawayen sun yi hasarar yankuna da dama a kudu da kuma yamma da birnin Damascus, amma har yanzu suna rike da wasu yankunan a gabas da birnin.

Babban inda ‘yan tawayen suka samu nasara cikin wannan lokaci, shine shine yankin arewa maso yammacin Syria, dab da bakin iyaka da kasar Turkiyya, inda mayakan adawa tare da goyon bayan sojojin Turkiyya suka fatattaki mayakan kungiyar Da’esh.