Sabon Filin Jirgin Sama Zai Sa Dakar Ta Zama Daya Daga Cikin Manyan Birane A Afrika

Tashar Jirgin kasa A Senegal

An gama gina filinjirgin sama a garin Dakar dake Senegal inda ake kokarin hadata da tashar jirgin kasa domin rage cunkoso a yankin tare da saukaka zirga zirga.

Gobe Alhamis ake sa ran za a bude sabon filin saukar jiragen sama da aka dade ana jira a Dakar babban birnin kasar Senegal.

An kammala dukkan ayyukan da suka kamata a wannan sabon filin jirgin sama mai suna Blaise Diagne, a bayan da aka kwashe sama da shekaru goma ana aikinsa.

Filin jiragen mai nisan kilomita 47, daga Dakar babban birnin kasar, ya hade da babbar hanyar zirga zirga ta kasar Senegal, kuma za a hade shi da tashar jirgin kasa da ake sa ran zata fara aiki a shekarar 2019.

Wannan sabon tsari na daga cikin shirin rage cunkoson jama’a a birnin da kuma mayar da Senegal cikin manyan biranen yammacin Afirka.