Dage Zaben Bai Da Alaka Da Batun Tsaro Ko Katsalandan Siyasa-INEC

Hukumar INEC Ta Yi Taron Manema Labarai Bayan Dage Zabe

Bayan ta sanar da dage zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun dokoki, hukumar zaben Najeriya ta INEC ta na gudanar da wani taro da masu ruwa da tsaki a babban zauren taron kasa da kasa dake Abuja, inda hukumar ta bada cikakken bayani a kan dalilan da ya sa ta dage zaben na yau Asabar.

Mahalarta wannan taron sun hada da masu sa ido na kasa da kasa da ‘yan jarida na kasa da kasa da suka shigo kasar kwanaki da dama da tsofaffin shugabannin Najeriya, sai kuma ‘yan takara da shugabannin jami’iyyu, wadanda suka bayyana rashin jin dadinsu ga wannan mataki na dage zaben.

Shugaban hukumar zabe ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu, da ya yi dogon jawabi a wurin taron, ya ce hukumar ta fara shirye shiryenta da wuri kuma ta hada hancin kayan aiki da malaman zabe tun da wuri amma daga bisani ta fuskanci kalubale da suka shafi karrakin kotu wanda a halin yanzu akwai kimanin karraki arba’in akan hukumar.

Shugaban na INEC ya ce rashin isar kayan zabe a wasu sassa na kasar, na cikin muhimman dalilan da suka yi sanadiyar dage zaben saboda kada a hana wasu ‘yan kasar kada kuru’unsu da dokar kasa ta basu ‘yancin yin hakan. Kana ya kuma tabo tabun konewar wasu ofisoshin hukumar suka yi, lamarin da ya shafin shirye-shiryen hukumar a wadannan yankuna.

Yayin da aka ba mahalarta damar tambayoyi, galibin ‘yan takara sun bayyanba damuwa ga wannan shawara da hukumar INEC ta dauka, sun kuma ce yakamata a nemi shawarsu kafin a dage zaben. Wasu ‘yan takara kuma sun ce dage zaben zai dora musu dawainiyar nemo kudade da zasu ci gaba da aiki kafin sabon mako da za a gudanar da zaben.

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta da INEC ta ce dage zaben ba shi da nasaba da batun tsaro ko kuma katsalandan din siyasa, ta yi haka ne saboda a bada dama kowa ya kada kuri’arsa. Ya kira ‘yan Najeriya su kwantar da hankalin su, hukumar sa za ta ci gaba da shirya zabe na gaskiya da adalci.

Ga hira da muka yi da Alheri Grace a zauren taron a Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

HUKUMAR TAYI JAWABI GA MASU RUWA DA TSAKI