Dage Zabe A Wasu Birane Uku A Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo

Hukumomi sun dage zaben a wasu birane uku dake Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, har sai watan Maris din badi.

Hukumomi a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, sun ce an dage zabe a wasu birane uku na kasar har sai watan Maris din badi, wato bayan an rantsar da sabon shugaban kasar.

A yau Laraba, hukumar zaben kasar ta Congo ta ce, ba za a yi zabe a biranen Beni da Butembo da ke Lardin Arewacin Kivu, da kuma birnin Yumbi da ke yammacin Lardin Mai-Ndombe.

Su dai biranen Beni da Butembo, suna fama ne da matsalar barkewar cutar Ebola tun daga watan Agusta, yayin da shi kuma birnin Yumbi ke fama da mummunan rikicin kabilanci.

Har ila yau, hukumar zaben kasar ta ce ba za a yi zabe a yankunan karkara da ke yankin Beni ba.

Duk da cewa an dakatar da gudanar da zabe a wadannan yankuna, zabe zai kankama a ranar Lahadi a sauran sassan kasar ta Jamhuriyar Dimokradiyar Congo a cewar hukumar.

A ranar 15 ga watan Janairun badi, za a fitar da sakamakon zabe na karshe, sannan a rantsar da wanda zai gaji shugaba Joseph Kabila, kwanaki uku bayan an fitar da sakamakon zaben.