Onarebul Isa Yaro Idris shugaban majalisar dokokin jihar Jigawa yace sun kafa dokar ce domin fadakar da juna da kuma tabbatar an yi aure bisa gaskiya ba tare da cutar da wani ko wata ba.
Dokar tayi tanadin hukumci mai tsanani ga duk wanda ya saba mata kama daga limamane da zasu daura aure zuwa saurayi da budurwa da zaurawa da ma ma'aikatan kiwon lafiya wadanda aka dorawa alhakin tantance lafiyar masu niyar daura aure.
Onarebu Sirajo Muhammad na majalisar dokokin jihar mai kula da ayyukan yaki da cutar kanjamau ta jihar yayi karin haske. Yace duk wanda ya daura aure ba tare da an yi gwaji ba akwai hukumci mai tsanani a kansa. Duk ma'aikacin kiwon lafiya da ya fallasa sakamakn gwajin da aka yiwa wani akwai tara da dauri da kuma kora daga aiki da za'a yi a kuma hanashi aikin kiwon lafiya a duk fadin Najeriya.
Wanda ya bada takardar bogi za'a cishi tarar nera miliyan daya kana a daureshi har na tsawon shekara biyu.
Gwamnati ta tanadi wuraren gwaji a duk fadin jihar kuma kyauta a ke yin gwajin.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5