Kundin Bajinta Na Guiness World Record Ya Tabbatarwa Da Hilda Baci Kambun Girki Mafi Tsawon Lokaci A Duniya

Hilda Baci

Kundin Nuna Bajinta na Duniya, World Guiness Records ya tabbatar da 'yar Najeriya mai dafa abinci Hilda Baci a matsayin wacce ta lashe kambun kwashe mafi tsawon lokaci tana girki babu kakkautawa.

Masu ba da kambun na Guiness World Record sun bayyana a wata sanarwar da suka sanya a shafinsu na yanar gizo cewa a ranar Talata, inda suka ce a halin yanzu, Hilda ce take rike da wannan kambu bayan da suka tantace hujjojin da aka gabatar musu a tsanake.

Bayan tantace dukkanin hujjoji, Guiness World Record ya tabbatar da Hilda Effiong wacce ake yi wa inkiya da Hilda Baci a matsayin wacce ta kwashe mafi tsawon lokaci tana girki babu kakkautawa a duniya cikin sa’o’i 93, da minti 11 GWR suka rubuta.

Idan ba a manta ba, matashiyr ‘yar Najeriyar mai shekaru 26 a duniya ta fara dafa abinci a ranar Alhamis 11 ga watan Mayun na bana kuma ta ci gaba da dafa abincin har zuwa ranar Litinin 15 ga watan mayun banan, inda ta dafa abinci kala dabam-dabam har 100 a cikin kwanaki hudun da ta kwashe tana girki.

GWR sun ce Hilda wace ta yi niyyar kafa tarihin girki na tsawon sa’o’I 100, ta gaza cima burin nata bayan da aka soke sa’o’I 7 cikin lokacin da ta kwashe tana girki bayan da ta zarce lokacin hutun da ya kamata ta dauka a farkon lokacin da ta fara girkin.

GWR sun ci gaba da bayyanai cewa, kamar yadda aka tanadarwa duk wanda zai shiga wannan gasa na girki na dogon zango, an amince ya dauki hutun minti biyar cikin kowani sa’a da zai yi yana girkin.

Idan ba ayi amfani da wandannan lokuta nah utu ba, ana iya tara su to amma kuma shine kawai lokacin da Hilda ta samu ta kewaya ko kuma ta dan rintsa a lokacin gasar.

‘Yar Indiya Lata Tondon ce ta samu kambun gasar ta baya a shekara ta 2019 bayan da ta kwashe sa’o’I 87 da minti 45 tana dafa abinci.