Da Yawa Iyaye Amurkawa Na Kashe Sama Da Biliyan $500 Akan 'Ya'ya

A wani bincike da kamfanin Merrill Lynch mai zaman kanshi ya fitar, wanda ya bayyanar da cewa, iyaye Amurkawa na kashe kimanin dalar Amurka biliyan $500 a kan yaransu matasa a kowace shekara.

Da yawa iyaye basa wani tanadi don tallafawa rayuwarsu a lokacin da tsufa yazo musu, shugaban bankin Amurka Mr. Merrll Lynch, ya shaidawa VOA ta sakon email cewar, iyaye kan kashe fiye da abunda suke tarama kansu akan ‘ya’yansu, ba tare da sun yima kansu wani tanadiba.

Akasarin kuden da sukan kashe ma ‘ya’yan nasu basu wuce kudaden haya na gida, kudin wayar salula, kai harma da na cin abinci.

A lokutta da dama saboda tsabar tausayin na 'ya'yen sukan shiga halin kuncin rayuwa, saboda kudaden da suka kamata su tara, don amfani da su a shekarun tsufa basu da su, ko kuma biyan kudaden asibiti.

Kimanin kashi 82 na iyaye Amurkawa sunce sukan kashe wadannan kudaden ne ga ‘ya'yan su, don samun zuri’a mai daurewa ga ‘ya'yan nasu.

A bangare daya kuwa, ana iyacewa iyaye masu haline kawai a kasashen Afrika kanyima ‘ya'yan su irin wannan gatan. Da yawa iyayen da basu da hali sai dai ‘ya'yan nasu su samo su basu, wanda hakan na iya shafar tattalin arzikin kasa.

A duk lokacin da akace ba’a samun kyauatatawa tsakanin iyaye da yara, wanda a karshe hakan zai iya haifar da rashin jituwa a tsakani daga bisani ma za’a ga rashin taimako a juna.