Da Gaske Ne Za a Kirkiri Wata Kasa Daga Najeriya, Kamaru?

Taswira Najeriya

Hukumar da ke kula da iyakokin Najeriya ta musunta rahotannin da ke nuni da cewa za a ƙirƙiro wata sabuwar ƙasa daga Najeriya da makwabciyarta Kamaru karkashin wani shiri na Majalisar Ɗinkin Duniya .

Rahotannin sun ce Najeriyar za ta rasa kananan hukukomi 24, sai a haɗa da wasu kananan hukumomi da ke ƙasar Kamaru domin a kafa wannan ƙasar.

Sai dai shugaban hukumar da ke kula da iyakokin kasar, Alhaji Adamu ya ce labarin ba shi da gaskiya ko kadan.

“Wannan labarin kamar yadda kuka jiyo haka muka jiyo kuma babu gaskiya a ciki. Wasu ne suke nemansu ta da hankalin mutane. Ba a taɓa ganawa tsakanin Shugaban Najeriya da na Kamaru kan wannan batu ba.” In ji Alhaji Adamu yayin wata hira da ya yi da VOA.

Wannan lamari ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin Najeriya, inda ake ikrarin cewa tun a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo aka kulla wata yarjejeniya tsakanin Shugaba Paul Biya da Majalisar Ɗinkin Duniya wacce aka sanya wa hannu a watan Maris na shekara ta 2003.

“Mun ba da shawara a gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro su yi bincike kan wadanda suka kawo labarin kuma a musu hukuncin da ya kamata.” Alhaji Adamu ya ce a lokacin da aka tambaye shi ko za a dauki mataki kan masu yada wannan labari.

Shi ma Amb. Hassan Tukur wanda ƙwararre ne kan harkar diflomasiya, wanda kuma yana da masaniyar yadda aka yi ƙuri’ar raba gardama a wancan lokaci ya ce labarin babu gaskiya a cikin lamarin.

“Shi wannan yanki daman yanki ne da yake ƙarƙshin Majalisar Ɗinkin Duniya. A ranar 11 ga 2 watan Fabairu na 1961 an yi zaɓen raba gardama, har kowane yanki ta zaɓi inda za ta zauna."

A cewar Amb. Hassan, wasu yankuna na Borno zuwa Taraba a Najeriya suka zaɓi su zauna a Najeriya, su ma Kamaru yankunan Buya da Bamenda suka zaɓi su zauna a Kamaru, Kudu masu yammacin Borno kuma suka zaɓi su zauna a Kamaru.

Kana rikicin Bakasi shi ya janzo har aka zauna tsakanin shuagabannin biyu don cimma matsaya a kan yankin.

Saurara karin bayani cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Da Gaske Ne Za a Kirkiri Wata Kasa Daga Najeriya, Kamaru?