DA DANGARI: Tarihin Masarautar Kanje, Jihar Nasarawa, Mayu 7, 2022

Bandiagara, Mali

Sadiq Abbas, na gidan Rediyo da Talabijin na jihar Nasarawa a Najeriya ya kai ziyara masarautar Kanje a karamar hukumar Awe da ke jihar ta Nasarawa don jin tarihinsa.

Washington, DC - Sarkin garin Kanje Aliyu Hashim, ya ce masarautar ta kafu ne tun a lokacin Usman Danfodiyo fiye da shekaru 200 da suka wuce.

Yakubun Bauchi, na daga cikin wadandan suka kafa garin, amma Munka’il Guraguri shi ne ya fara sarauta karon farko a garin.

Garin Kanje ya kunshi kabilun Jukunawa, Kanuri, Katsinawa da sauransu. Kuma ana yi masa kira da “Kanji Kangiya Kan Kura.”

Garin ya yi suna ta fannin jihadi a lokacin Usman Danfodio, bayan haka ya kuma shahara wajen noma da farauta.

Saurari cikakken shirin cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

DA DANGARI: TARIHIN MASARAUTAR KANJE, JIHAR NASARAWA